1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An bude rumfunan zabe na 'yan majalisar dokoki a Togo

April 29, 2024

Al'ummar Togo sun isa rumfunan zabe domin kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar, bayan kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulki da 'yan adawa ke cewa hakan wata manufa ce ta Faure Gnassingbe na tazarce.

https://p.dw.com/p/4fJWr
Wata mai kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin Togo, a birnin Lome
Wata mai kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin Togo, a birnin LomeHoto: Emile Kouton/AFP

A bisa sauye-sauyen da 'yan majalisar suka yi wa kudin tsarin mulkin Togo, za a zabi shugaban kasa  sau daya a  wa'adin mulki na shekaru hudu, wanda za a iya sabunta shi sau daya, daga bisani 'yan majalisa ko kuma jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar za ta ci gaba da nada shugaban kasa.

Karin bayani: Karar Togo kan gyara ga kundin tsarin mulki 

A zaben na yau litinin al'ummar kasar ta Togo zasu zabi 'yan majalisa 113 da kuma mataimakan magadan gari 179 daga shiyyoyi biyar na kasar da kansiloli; wadanda su ke da alhakin zabar 'yan majalisar dattawan da aka kirkira a kasar.

Karin bayani:  An saka ranar zabukan Togo da aka dage bayan rudanin siyasa

Shugaba Gnassingbe, ya lashe zaben shugaban kasar sau hudu da saura wa'adi daya na zaben 2025 zai kare wa'adin mulkinsa ba tare da tazarce ba, to amma wannan sabon tsarin na firaimista da 'yan majalisar dokokin kasar suka bujiro da shi zai bawa shugaban ci gaba da kasancewa kan karagar mulki har mahadi ka ture.

Karin bayani:  An haramta zanga-zanga a Togo

Shugaban ya gaji mahaifinsa ne Gnassingbe Eyadema wanda ya shafe shekaru kimanin 40 yana mulkin kasar ta Togo da ke yammacin Afrika.